Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya gargadi al’umma da su guji baiwa wadanda ake zargi da aikata muggan laifuka kariya a tsakanin su yayin da gwamnati ke kokarin magance matsalar rashin tsaro a fadin jihar.
El-Rufai ya yi wannan gargadin ne a ranar Larabar, a lokacin da ya ziyarci Sarkin Kagoro, Mista Ufuwai Bonet, a fadarsa da ke karamar hukumar Kaura, domin jajantami shi kan harin da aka kai a yankin kwana-kwanan nan.
Hakan na zuwa ne kasa da ‘yan kwanaki bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta Abuja zuwa Kaduna.
“Abun takaici ne kannyadda al’ummomi ke kare masu aikata laifuka da ke zaune a cikinsu. Akwai masu laifi a kowace kabila da kowane addini.
“Idan muna son kawo karshen irin wannan matsalar (rashin tsaro), dole ne mu kasance a shirye mu rabu da wadanda muke zargi da aikata laifuka ko da ‘ya’yanmu maza ne mata,” inji gwamnan.
A cewarsa, zaman lafiya za a samu ne kawai idan al’ummomi suka mutunta hukumomin da aka kafa tare da kai rahoton wadanda ake zargi ga hukumomin tsaro.
“Wannan ita ce hanya daya tilo da za mu iya rayuwa cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.
El-Rufai ya bukaci sarakunan gargajiya da su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kansu na samar da shugabanci.
“Idan har hukumomin gargajiya da sauran jami’ai ba za su iya samar da shugabanci ba, to za mu iya murkushe su mu mika ragamar shugabancin ga matasa idan har hakan ne zai kawo zaman lafiya.
“Ina so in yi kira gare da ku da ku tashi tsaye wajen ganin kun gudanar da ayyukan ku na jagoranci kamar yadda ya dace, kuma kun sanar da mu wadanda ke da hannu wajen aikata laifuka domin mu magance su,” in ji shi.