By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Kaduna ta nada Kwamitin Ziyara na mutum bakwai na jami’ar jihar KASU, shekaru biyar tun bayan da aka kafa bangarorin ziyara na karshe ga wasu manyan makarantu mallakar gwamnatin jihar.
Mai bada shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa na gwamnan, Mista Muyiwa Adekeye, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, a Kaduna cewa nadin yana aiki ne da ikon Gwamna Nasir E-Rufai a matsayin mai ziyartar cibiyar.
Adekeye ya bayyana Dr Abba Gumel a matsayin shugaban kwamitin, tare da Ibrahim Khalilullahi Zubairu, Dakta Dahiru Sani, Andrew Bobai Suku, Mariya Abdulkadir, Farfesa Abu Mallam da kuma Farfesa Isa Abubakar, a matsayin membobi.
”Sharuɗɗan kwamitin sun haɗa da,bada shawarwari don tabbatar da cewa manhaja da al’adun KASU na gudana don shirya ɗalibai dai dai da buƙatun zamani, ” in ji sanarwar.