A wani mataki na ganin an samu maslaha dangane da dambarwar gwamanti da yan kwadago a Jihar Laduna,Gwamnonin shiyar arewa a kasar nan sun bukaci bangarorin biyu na Jihar Kaduna wato ɓangaren gwamnati da na kwadago da su kai zuciya nesa ta hanyar zama teburin sasantawa.
Shugaban Kungiyar wanda shine gwamnan jihar Pilato Simon Bako Lalong shi ya mika wannan bukata cikin wata sanarwa mai dauke da sanya hannun Daraktan watsa labaran sa da kuma harkokin jama’a Dakta Makut Macham.
Ya ce Gwamnonin arewa sun kadu matuka bisa wannan al’amarin musamman irin halin da al’umma za su shiga sakamakon hakan.
Lalong ya ce hanya daya da za a samu maslaha ita ce kawai zaman teburin sulhu, ba wai tada jijiyoyin wuya ba.
Ya kuma yi amfani da damar wajem kira ga ƴaƴan Ƙungiyar kwadagon da su kai Zuciyar su nesa ko da wasu yan baranda za su takale su, domin maida martani ka iya haifar da abin da na sani.