Kungiyar shugabannin addinin Kirista karkashin inuwar United Pastors for Change ta yi kira ga gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da jami’an tsaro da su kara himma wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar da sauran sassan yankin Arewa a sabuwar shekara.
Yayin da yake mayar da martani kan tabarbarewar tsaro a arewacin kasar, kungiyar ta bakin shugabanta, Apostle David Adeniran, ya ce duk da cewa gwamnati da hukumomin tsaro suna bakin kokarinsu wajen ganin an shawo kan matsalar ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane, amma akwai bukatar a kara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
A wani taro da kungiyar ta shirya, Apostle Adeniran ya bada tabbacin cewa malaman addinin za su ci gaba da baiwa gwamna El-Rufai goyon baya domin ganin gwamnatin sa ta samu nasara a fannin samar da shugabanci na gari da zaman lafiya ga al’ummar jihar Kaduna.
Adeniran ya bukaci ‘yan siyasa da su ci gaba da yin ado da kuma inganta zaman lafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya, kamar yadda kuma ya ce dole ne shugabannin addinai su yi wa’azin hakuri, hadin kai, da zaman lafiya, kuma kada su yi wa ikilisiyoyinsu mummunar fahimta a kowane mataki.
Dangane da abin da ya sanar da yanke shawarar shirya taron tattaunawa na karshen shekara, Adeniran ya ce “an shirya taron ne domin fadakar da jama’a game da wasu manufofin gwamnati.
“Sau da yawa, ana yiwa mutane mummunar fahimta game da manufofin gwamnati, kuma an ce jahilci na da hadari, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa aka shirya taron,” in ji shi.
A nasa jawabin, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani, wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa kan harkokin addinai Hamza Muhammed, ya yabawa wadanda suka shirya taron na hada kan masu ruwa da tsaki domin amfanin jihar da ma kasa baki daya.
Hakazalika, dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Kudu a majalisar wakilai ta kasa, Hon. Mukthar Ahmed Monrovia ya ce shugabancin Gwamna Nasir El-Rufai ya yi kyakkyawan aiki ta hanyar mayar da jihar zuwa matsayi kyakkyawa.
Dan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa, Samuel Yohana ya bukaci al’ummar jihar Kaduna da su sanya hannu kan ajandar kawo sauyi na gwamna El-Rufai tare da rungumar zaman lafiya domin ci gaban jihar.