A ranar Talata ne mazauna Kakuri, Nasarawa, Kurmi Gwari, Angwan Tarke, Romi, suka dunga shigewa cikin gidajensu, yayin da wasu suka dunga neman mafaka, bayan da suka ji karar jirgin helikwafta na wucewa ta sama.
Mazaunan da tun farko suka shagaltu da gudanar da al’amuransu na yau da kullun, sun fake ne a wasu wurare, suna tunanin cewa wata kila ‘yan fashin suka yi amfani da wata dabara, domin kai musu hari.
Sun ce ba za su iya aminta da kowa ba, ciki har da gwamnati ko jami’an tsaro, suna masu zargin cewa galibin hare-haren suna samun goyon bayan wasu mutane masu fada a ji a kasar nan.
Wani mazaunin Kurmi Gwari Shu’aibu Murtala ya ce a lokuta da dama jiragen sama masu saukar ungulu na shawagi zuwa yankin Arewa ko Kudancin garin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Peter Obi Ba Ya Goyon Bayan IPOB—Baba Ahmed
Ya ce wasu mazauna yankin da suka ji karar jirgin mai saukar ungulu, sai suka bar abin da suke yi, suka shiga cikin gidajensu saboda fargabar harin yan bindiga.
Ya kara da cewa, a ko da yaushe suna nuna fargabar ‘yan bindiga su kai musu hari ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu.
Wata mazauniya, Maryam Yusufu ta ce sun sha jin labarin hare-hare ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu, ko kuma sojojin sama na kai hare-hare a kauyuka bisa kuskure, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda suke tsammanin yan ta’adda ne.
John Bulus, wani mazaunin Sabon Tasha ya ce, “Ban san abin da wadannan mutane suke nema ba a kodayaushe, a kusa da muhallinmu, saboda ba mu kusa da dajin.
Ya ce a duk lokacin da ya ji karar jirgin mai saukar ungulu, sai ya hankalin shi ya tashi tare da neman inda zai buya, saboda tsoron kada a kai masa hari.
Har ila yau, Uwargida Juliana Moses, matar aure kuma mazauniyar garin Kakuri, ta ce ya kamata gwamnatin jihar ta rika wayar musu da kai kan duk wani mataki da za ta dauka kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.
A cewarta, saboda halin da jihar Kaduna ke ciki, ya kamata a rika sanar da jama’a abubuwan da ke faruwa.
Sai dai ko da aka tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin saman Najeriya bai dauki kiran da aka yi masa ba domin bai da martani kan lamarin.