By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka guda uku a garin Kafanchan hedikwatar karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, hanyoyin sun hada da titin Katsina, titin Dan haya da titin fadar sarki, wanda aka gina a karkashin shirin sabunta biranen Kafanchan na gwamnatin jihar.
A karkashin shirin sabunta birane na gwamnatin jihar, an sake gina tituna 21 masu tsawon kilomita 26.3 ko dai an sake gina su, ko kuma a fadada su ko kuma aka yi musa duka biyu wato ginasu baki daya a Kafanchan, kan kudi Naira biliyan 12.8.
Shugaba Buhari tare da gwamnan jihar, Malam Nasir Elrufai, sun zagaya a sabbin hanyoyin da aka kaddamar, a daidai lokacin da dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsu.
Daga nan ne shugaban ya zarce zuwa fadar Sarkin Jema’a da ke Kafanchan domin yin mubaya’a, daga nan kuma ya wuce Kaduna babban birnin jihar domin kaddamar da wasu ayyuka.