By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar ilimin bai daya ta jihar Kaduna ta tsunduma cikin shirin mayar da yaran almajirai 10,500 da aka dawo dasu zuwa makaranta.
Shugaban hukumat ta SUBEB, Alhaji Tijjani Abdullahi ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Alhamis a Kaduna.Yace za a bayar da tukaucin ne ga jihohin da suka cimma burin yin nasarar shigar da yaran da basa zuwa makaranta da kuma mayar da yaran almajirai da sauran su zuwa makaranta.
A karkashin shirin SUBEB na bayar da ilimi na asali ga kowa, ta kuma shirya komawa makaranta ga ’yan mata 24,000 da yara marasa galihu 16,500 a kananan hukumomi 14 na jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa BESDA wani tallafi ne na Bankin Duniya ga Najeriya na dalar Amurka kimanin naira miliyan 611 don mayar da yara makaranta.
Masu ruwa da tsakin dai zasu yi aiki a sahun gaba a harkokin mayar da yaran makaranta su ne; Sakatarorin ilimi, jami’an wayar da kan jama’a, shugabannin zamantakewa da wayar da kan jama’a na kananan hukumomi 14 da kuma shugabannin ilimi da dai sauransu.
Abdullahi wanda shine ya wakilci Daraktan tabbatar da inganci Malam Tanko Aliyu yace kananan hukumomin da aka zabo su ne wadanda ke da almajirai masu tarin yawa.A cewarsa, kudaden da aka amincewa da shirin na mayar da yaran Makaranta gwamnatin jihar za ta biya su idan ba a yi aikin ba.
Masu ruwa da tsakin zasu kuma hada yaran da suka halarci makaranta domin tantancewa a saukake daga waɗanda basu yi ba, da sauran dabaru da dama.
Kananan Hukumomin su ne; Birnin Gwari, Igabi, Ikara, Kachia, Kaduna-ta kufu, Kagarko, Kauru, Kubau, Kudan, Soba, Makarfi, Giwa, Zaria da kuma Makarfi a matakin farko na wayar da kan jama’a da bayar da shawarwari kan mayar da yaran Almajirai da sauran su zuwa makaranta.