By Abbas Yakubu Yaura
A daren jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a gundumar Zango Urban dake karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Wani mazaunin Zango, Malam Isa Tela, wanda ya zanta da jaridar Aminiya yace: “An fara harbe-harbe ne da misalin karfe 8:00 na dare a wani wuri dake kusa da gidan mai na garin, kafin daga bisani suka kewaye garin ta kowane bangare.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa daga baya rundunar sojoji sun tarwatsa maharan.
Idan za’a iya tunawa an kashe mutane takwas a wasu hare-hare da aka kai a kauyukan Zangon Kataf a makon jiya.