By Ishaq Dabai
Shugaban Hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC reshen jihar kaduna Mr Hafiz Mohammed a ranar Talata ya tabbatar da mutuwar mutane 12 biyo bayan hadarin mota akan hanyar kaduna zuwa Abuja.
Mohammed ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN hadarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Toyota Hayis mai dauke da fasinjoji 18.
Yace hadarin ya afkune a ranar litinin da misalin karfe 12:00 na rana kuma yayi sanadiyyar jikkatar mutane shida daga cikin motar, inda sha biyu daga cikin fasinjojin suka rasa rayukansu a sakamakon faduwar motar a Nasarawar Doka kusa da titin Kaduna zuwa Abuja a karamar hukumar Kachia.
Hatsarin ya faru ne a sakamakon fashewar tayar motar a kan titin Zariya zuwa kaduna.