Masa zanga-zangar kafa kafa kasar Yarbawa sun shafa wa kansu ruwa inda suka ƙi fitowa Gani Fawehinmi Park dake Ojota na birnin Ikkon jihar Legas, inda nan ne aka tsara gudanar da zanga-zangar.
Kawo yanzu dai da muke hada muku wannan rahoto babu ko tsinke gurin zanga-zangar, wacce aka shirya gudanarwa daga karfe 9 na safe.
Idan ba a manta ba da ma kungiyar Yarbawa ta Yoruba Self-determination Groups Ilana Omo Oodua karkashin Sanata a jamhuriya ta farko wato Banji Akintoye ta ce ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar.
To sai dai kawo yanzu za a iya cewa masu zanga-zangar sun shafa wa kansu ruwa kenan ta hanyar kauracewa zanga-zangar, kuma hakan ba zai rasa nasaba da dakarun da aka jibge a birnin ba.
Kokarin da Jaridar Punch ta yi don samun Kakakin Shugaban ranjin kafa kasar Yarbawar Sunday Igboho mai suna Olayomi Koiki kan dalilin kin fitowa zanga-zangar abin ya ci tura.