Jami’an tsaro a birnin Legas sun wargaza taron Masu zanga-zangar kafa kasar Yarbawa a Gani Fawehinmi Park dake Ojota na birnin Ikkon jihar Legas.
Kawo yanzu dai da muke hada muku wannan rahoto ana can ana ta kai ruwa rana tsakanin masu zanga-zangar da kuma jami’an tsaron.
Da ma dai an shirya fita zanga-zangar ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Asabar, to amma masu zanga-zangar ba su fito a kan lokaci ba.
Idan ba a manta ba da ma kungiyar Yarbawa ta Yoruba Self-determination Groups Ilana Omo Oodua karkashin Sanata a jamhuriya ta farko wato Banji Akintoye ta ce ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar, ko da yake jami’an tsaro sun nuna karfin iko wajen tarwatsa su.
To sai dai kawo yanzu babu adadin masu zanga-zangar da aka kama ko kuma aka harbe.
Kokarin da Jaridar Punch ta yi don samun Kakakin Shugaban ranjin kafa kasar Yarbawar Sunday Igboho mai suna Olayomi Koiki game da zanga-zangar abin ya ci tura.