Kungiyar Kwallon Kafa ta Leeds United ta sallami kocinta Jesse Marsch. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Kungiyar ta sallami kocin ne biyo bayan rashin nasarar da take samu a baya bayan nan.
KANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: An Jibge Tarin Jami’an Tsaro A CBN
Leeds ta saki wani takaitaccen sanarwa na sallamar kocin a yau Litinin, inda ta bayyana cewa, Za ta sanar da wanda zai maye gurbin Jesse March cikin makon nan.
Har kawo yanzu kungiyar Leeds ta gaza lashe ko wasa daya a gasar Firimiya tun a ranar 5 gawatan Nuwanban shekarar nan.
Kana mamallakin kungiyar kuma dan kasar Amurika ya karbe ta ne daga hannun Mercelo Bielsa inda yanzu kuma yake da ra’ayin sallamar da ita.
Rashin nasarar da suka yi a hannun Nottingham Forest ranar Lahadi ya sanya kungiyar ta koma mataki na 17 a teburin gasar ta Firimiya.
A wani labarin kuma, Karancin Sabbin Kudi Ya Sa APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Tinubu
Jam’iyyar APC reshen Oyo ta tabbatar da dage taron gangamin yajin neman zaben Dan takaran shugaban kasanta da aka shirya gudanarwa a dakin taro na Mapo Hall dake Ibadan a ranar Talata. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ta ce kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa karkashin jagorancin Gwamna Simon Lalong ya dauki matakin ne saboda halin da al’ummar kasar nan ke ciki.