Sojoji

Kai ‘Bera Ne Kawai- Martanin Hedikwatar Tsaro Ga Shekau

Da hedikwatar tsaro ke mayar da martani ga kalaman da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi, ta bayyana Shekau a matsayin Beran da ya shige rami ya boye ba ya iya fuskantar rundunar sojin Nijeriyar.

Mukaddashin Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron, Janaral Onyema Nwachukwu shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ‘yan ta’adda kamar shugaban Boko Haram ba za sui ya korar rundunar sojin Nijeriya a arewa maso gabashin Nijeriya ba.

Ya ce rundunar tsaron za su ci gaba da aikinsu wajen ‘yanto wadanda Boko Haram ta kama, sannan ya ce ba su da bukatar tattaunawa da ‘yan ta’adda. Ya ce Shekau ba shi da karfin da zai iya fuskantar rundunar sojin, shiyasa yake buya da gudu kamar Bera, yana kuma amfani da fararen hula wajen kare kanshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *