Kai fa ba wani Ɗan Siyasar Kirki bane a Najeriya – Okowa ya caccaki Tinubu
Gwamna Ifeanyi Okowa ya yi Allah-wadai da caccakar da Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu ya yi wa Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.
Mataimakin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP ya shaidawa Tinubu cewa shi ba wani ɗan siyasa ba ne a Najeriya daya fi kowa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Buni ya ayyana hutun ranar Litinin domin murnar sabuwar shekarar Musulunci
Gwamnan yana maida martani ne kan kalaman Tinubu na cewa abokin takararsa Sanata Kashim Shettima ya fi.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olisa Ifeajika ya fitar, Okowa ya shawarci Ɗan Takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ya bar yakin Neman Zabe.
Shugaban na Delta ya shawarci Tinubu da ya duba tarihinsa a siyasa, Majalisa da kuma harkokin mulki.
Okowa ya tuno da hirar da Atiku ya sake nanata cewa Jigon jam’iyyar APC na son zama abokin takarar sa a shekarar 2007.
Ya ce maimakon ya mayar da martani, Tinubu ya zage shi, yana mai cewa abokin takararsa ya fi na Atiku.
“Mun san Sanata Bola Tinubu a matsayin dan siyasa nagari kuma tsohon gwamnan jihar Legas.
“Amma muna sa ran ya san cewa akwai wasu ‘yan siyasa da suke da tsayin daka kuma masu nagarta, masu kishin kasa kuma suka yi kokarin zama ‘yan jiha.
“Idan Tinubu yana ganin yana da kyau, bai kamata ya fayyace cewa ba za a samu wasu mutanen da suka yi kyau ko ma sun fi kyau a siyasa inda ya samu ci gaba ba.
Sanarwar ta ce ” zabinsa ne ya zabi abokin takararsa kan kowane irin sharudda da yake da shi”.
Ya sanar da Tinubu cewa dokar kiwon lafiyar kasa ta fito ne daga kokarin Okowa lokacin yana Majalisar Dattawa.
Ifeajika ya shawarci dan Takarar jam’iyyar APC da ya fuskanci takararsa… kuma ya bar yaƙin neman zabe da zagi.
Sanarwar ta kara da cewa “Ya kamata Tinubu ya rika tattaunawa kan batutuwan da suka shafi rayuwar jama’a, ba wai tattaunawa kan daidaikun mutane ba.”