Wani matashin yaro dan shekaru 15 da haihuwa ya shiga komar ‘yan sanda bayan da aka kama shi da laifin yin lalata da yarinya ‘yar Shekaru 3 a duniya.
Wani wanda ya ganewa idonsa yace lamarin ya afku ne a anguwar Osi Ekiti, dake karamar hukumar Ido Osi dake jihar Ekiti.
Lamarin ya faru ne a yayin da matashin ya ja hankalin karamar yarinyar da cin-cin zuwa dakinsa wanda a nan ne ya samu damar yin wannan aiki na assha.
https://dimokuradiyya.com.ng/fyade-gwamna-obaseki-ya-umarci-a-yi-bincike-akan-kisan-omozuwa/
Wasu mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewa an sanar da hukumar’yan sanda, kuma al’amarin yaje har gaban matar gwamnan jihar, wato Erelu Bisi Fayemi, wanda ta bada umarnin yin bincike tare da hukunta mai laifin.
Yayin da kamfanin dillancin labarai ya tuntubi kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar, Sunday Abutu ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace matashin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.