By Abbas Yakubu Yaura
An yi wasan kwaikwayo a babbar kotun jihar Ebonyi, a ranar Laraba, lokacin da sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na jihar, Mista Chika Nwoba, ya fadi a harabar kotun, a Abakaliki, yayin da ‘yan sandan ke shirin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ne suka shigar da shi harabar kotun da misalin karfe 2:45 na rana amma an canja lokacin zaman kotun saboda yanayin lafiyar Nwoba.
Bayan faruwar lamarin ne jami’an ‘yan sanda suka yi gaggawar fitar da shi daga harabar kotun, daga bisani kuma suka dawo da shi kotu, domin a bar zaman kotun ya fara aiki.
A lokacin da wakilinmu ya isa harabar kotun a karo na biyu, Nwoba na cikin motar ‘yan sanda da ke sintiri, yana jiran a gurfanar da shi a gaban kotu.