Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Zailani ya musanta labarin dake cewa ‘yan majalisar jihar sun fara wani yunkurin tsige gwamna Nasir El-Rufai kan zargin cin hanci da rashawa, kamar yadda AIT Live ta rawaito.
A wata sanarwa da kakakin majalisar ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana labarin a matsayin na hannun ‘yan adawa da makiya na ci gaban dangantakar da ke tsakanin majalisar da bangaren zartaswa na gwamnati a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Hadimin Atiku Ya Caccaki Hukumar INEC Kan Tattara Sakamakon Zaben 2023 Da Hannu
Ya ce mawallafin labarin ya yi nisa ne don hana al’ummar jihar Kaduna ribar sharbar dimokuradiyya da suke amfana da kyakkyawar alaka ta aiki.
“Zailani ya bayyana rahoton, wanda kuma ya ce dangantakar da ke tsakanin gwamnan da shi ta yi sanyi, a matsayin tunanin marubutan da watakila masu daukar nauyinsu.”
A wani labarin kuma Mambobin APC Da Wasu Jam’iyyu Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP A Bauchi
Magoya bayan jam’iyyun adawa ta APC, NNPP da PRP a kananan hukumomin Kirfi da Alkaleri na jihar a karshen mako sun fice daga jam’iyyun su zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
Da yake karbar wadanda suka sauya sheka, Gwamna Bala ya jinjinawa jajircewarsu kan yadda suka bar tsoffin jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar PDP mai mulki, ya kuma yi alkawarin daukar su domin samun nasarar jam’iyyar a babban zaben badi.