Kakakin Majalisar Nijeriya, wato Femi Gbajabiamila na jam’iyyar APC a ziyarar a ya kai a jiya Litinin a garin Katsina, ya kai ziyara makarantar Sakandare dake Kofar Sauri.
Kakakin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa: a ziyarar da ya kai ya shiga Aji inda ya karantar da wadansu daliban makarantar Sakandare dake Kofar Sauri a jihar Katsina.
Ya yi alkawarin gina musu azuzuwa da kuma daukar nauyin karatun wanda ya fi kowa kwazo cikin daliban makarantar a duk shekara.