By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya, a ranar Litinin din data gabata ya gayyaci kamfanin Avic Engineering Limited, dan kwangilar dake kula da aikin gina filin jirgin sama na Gusau.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dokokin jihar Zamfara Mustapha Jafaru-Kaura ya fitar.
Magarya wadda ya jagoranci shugabannin kwamitocin gidaje daban-daban zuwa wurin da aka gudanar da aikin, ta gayyaci dan kwangilar domin bayyana dalilin da ya sa aikin ke tafiya a hankali.inda Kakakin majalisar yace tawagarsa tana wurin aikin ne a matsayin wani bangare na aikin majalisar kamar yadda yake a sashi na 128 na kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, kamar yadda aka yi masa kwaskwarima.
“Kudin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya baiwa majalisar dokokin jiha damar gudanar da ayyukan sa ido kan ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa.”
Magarya ya umarci kwamishinan gidaje da raya birane da ayyukan sufuri da kuma mai ba da shawara kan aikin, B.J. Aeronautics, don bayyana a gabansa don fayyace dalilin jinkirta aikin.inda Shugaban majalisar yace ganawarsa da masu ruwa da tsaki zata samar da mafita ga tsaikon aikin.
Tun da farko kwamishinan gidaje da raya biranen jihar Alhaji Ahmad Muktar Gusau a lokacin da yake gudanar da jawabi a zagayen aikin ya bada tabbacin cewa ba za a tauye ingancin aikin ba.Kwamishinan yace an jinkirta aikin ne saboda karancin kudi da kuma matsalar tsaro da kuma lokacin damina a jihar.
Sai dai ya tabbatar wa shugaban majalisar cewa ma’aikatar za ta tabbatar da cewa an kiyaye daftarin kudirin.A cewar Kwamishinan, ma’aikatar ta ci gaba da kai ziyarar aikin mako-mako don tabbatar da bin ka’ida.
Gwamna Bello Matawalle, yayin da yake duba aikin a watan Mayu, yace filin jirgin na Cargo zai fara aiki kafin karshen shekarar 2021.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa idan zaku iya tunawa tsohon Gwamnan Mahmud Aliyu Shinkafi shine wanda ya kaddamar da aikin tun a shekarar 2008, kan kudi na farko na kwangilar aikin Naira biliyan 10, amma wanda ya gaji gwamnatin Gwamna AbdulAziz Yari bai ci gaba da aikin ba a tsawon shekaru takwas da yayi yana mulki.