Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hajiya Mowa Sufi Yakasai, kakar Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP, ta rasu.
Hajiya Yakasai mai shekaru 103 ta rasu ne bayan tayi wata gajeriyar rashin lafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugabannin Taiwan ‘Yan Aware Ne, Hada Kai Da Baki Zai Haifar Da Mutuwa – China
Kakakin Dan Takarar Gwamna Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai wanda Jaridar Daily News 24 ta samu.
Tare da kaushin zuciya da mika wuya ga ikon Allah, muna cikin alhinin rasuwar Hajiya Aishatu Ahmad Sufi.
Marigayiyar wacce ta kasance kaka ce ta uwa ga dan takarar Gwamna na jam’iyyar NNPP mai rike da tutar gwamnan jihar Kano 2023 Engr.Abba Kabir Yusuf.
Hajiya Mowa kamar yadda aka fi sanin ta, ta rasu da sanyin safiyar yau Juma’a 12 ga watan Agusta 2022 daidai da 14 ga watan Muharram 1444H a asibitin koyarwa na malam Aminu Kano.
Za’ayi Sallar Jana’izarta a fadar Sarkin Kano bayan Sallar Juma’a.
Daga cikin ‘ya’yanta akwai tsohon sakataren ilimi a kwalejin Aminu Kano AKCILS, Ibrahim Abubakar Aminu.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama daga cikinsu akwai likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Dakta Atiku Musa.