Takaddamar da ta kunno kai tun bayan da aka bayar da sanarwar gano wadansu yara da ake zargin sace su aka yi daga birnin Kano na arewacin Najeriya ta ci gaba da ruruwa.
A baya-bayan nan dai wasu kalamai da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya furta ne suka haddasa ce-ce-ku-ce.
Yayin wani jawabi da ya yi a wajen wani taro a birnin na Kano, Sarki Sanusi ya ce, “Duk yaran nan da ake cewa an sace, kuma ana cewa Sarki bai yi magana ba, mun riga mun yi bayani—tun da aka fara maganar yaran nan na Onitsha, muka yi magana da Obi of Onitsha, kuma muna sane da halin da ake ciki kuma da binciken da ake yi”.
Daga nan ne Sarkin ya ce idan bera na da sata, to daddawa ma na da wari:
“Amma kafin a zo kan wadanda aka ce sun sace mana yara—duk ana ta zage-zage, sun sace mana yara—mun ji, sun yi laifi. Amma shin wanda ya saci yaron nan cikin gidanka ya shigo ya sace shi? Ko kai ne ka bar danka dan shekara uku ya fita yana yawo a kan titi ba ka ma san inda yake ba?
“Ni na fada—na san sanda aka kama wasu aka kawo kara gaban Sarki—a lokacin cewa na yi da ni nake da gwamnati, da duk mahaifansu sai na daure su.
“Kuma har na ce a nemi kwamishinan ‘yan sanda, shin ba mu da doka ne da ake cewa criminal negligence? …Laifi a wajenmu yake, mu ne masu laifi.”
Martanin Sarki
Sarkin ya yi wadannan kalaman ne dai bayan ce-ce-ku-ce da aka yi ta yi a Kano, game da rashin jin martaninsa kan batun.
A karshen watan Oktoba ne rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ce ta ceto wasu yara tara waɗanda ta ce wasu ‘yan kudancin ƙasar ne suka sace suka kuma sayar da su a jihar Anambra, tare da sauya musu suna da addini.
Kalaman Sarkin dai sun janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman ma Kano inda wasu ke cewa abin da Sarkin ya fada gaskiya ne yayin da kuma wasu ke cewa har cikin gida aka shiga aka ɗauki ɗaya daga cikin yaran.
Hidaya Salisu Ahmad ta goyi bayan kalaman Sarkin inda ta ce “Gaskiya wannan maganar ta yi daidai saboda za ka ga idan iyaye suna hayaniya sai a ce wa yaro jeka waje ka yi wasa kuma shekarunsu bai kai su fita su kadai ba.”
“A tunanna, a ce wai wannan laifin iyaye ne, wannan kuskure ne saboda wani ya tura ɗansa makaranta amma an dauke shi,” in ji wani magidanci a Kano.
A ranara 31 ga watan Octoba gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin jin bahasi kan sace yaran bisa karkashin jagorancin Mai Shari’a Wada Umar Rano.
Tuni kwamitin ya fara zamansa a kotun da ke Miller Road, bayan kira ga iyayen yaran da kuma masu ruwa da tsaki domin gabatar da bayanai. Kamar yadda rahoton Bbc Hausa ya tabbatar.