By Abbas Yakubu Yaura
Shugaba bulaliyar majalisar dattawa ta 9, Sanata Orji Uzor Kalu, ya yi watsi da ra’ayin cewa yana aiki tare da wasu domin dakile babban taron jam’iyyar APC mai mulki a ranar 26 ga watan Maris.
A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kan sa, Kalu ya bayyana zargin da wani tsohon darakta-janar na kungiyar cigaban gwamnonin (PGF), Dakta Salihu Lukman ya yi masa a matsayin abin takaici.
Ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saurari bangarorin biyu domin jam’iyyar ta samu nasara tare.
Tsohon gwamnan jihar Abia ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki da su kiyaye maganganunsu “a wannan lokaci na kalubale da rashin fahimta”.
Kalu ya ce, “ idan za a iya tuna cewa a ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2021, na yi kira ga jam’iyyar da mambobin kwamitin tsare-tsare na riko da na musamman da su duba yiwuwar dage babban taron kasa da aka shirya yi a watan Fabrairu.
“Na yi gargadin cewa gudanar da babban taron a watan Fabrairu ba tare da sasanta ‘yan kananan husuma da suka taso a lokacin taron ba zai kai ga gallazawa.
“Na damu cewa ƙirƙirar ƙungiyoyi, waɗanda suka musanta nasarar jam’iyyar a jihohi da dama a zaɓen da suka gabata na iya maimaita kansu. Don haka na yi kira da a warware rikicin cikin lumana kafin gudanar da babban taron.
Sannan babu wani shugaba mai zaman lafiya da dabara da zai goyi bayan mummunan yanayin da zai sake faruwa.”
Comments 1