Jami’an Tsaro a Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Gwamnatin Tarayya dake Jihar Kogi sun yi nasarar yin ram da wani dalibin Diploma ajin karshe dauke da bindiga Kirar Pistol.
Da yake gabatar da dalibin mai Suna Shehu Tanimu Muhammad Mai kuma lambar rajista 2018/ND/PAD/170 ga manema labarai, Babban Hafsan Tsaron Kwalejin ya tabbatar da cewa a jiya Juma’a ne aka chafke dalibin dauke da bindigar hadi alburusai masu rai guda biyar.
Ya ce wannan nasara ya biyo bayan baza Koma ne da jami’an tsaron suka yi bisa samun rahotannin cewa akwai dalibai masu shirin harba bindiga bayan sun kammala jarabawar su ta karshe.
Ya kuma ce baya ga wannan dalibi, akwai wani Keke NAPEP da jami’an tsaro suka chafke da ake zargin cewa suna yunkurin harba Bindiga a wajen Makarantar, a wani mataki na nuna murnar kammala Jarabawa.
A yanzu haka dai ya ce za a damka dalibin ga jami’an tsaron da suka kamata don zurfafa bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
Da Jaridar Daily Trust ta tuntubi kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar Kogi ASP Williams Ayah don ji ta bakin shi abin ya ci tura, domin ya gaza daukar kiraye-kirayen da aka yi mishi tare da amsa sakon kar-ta-kwana.