By Abbas Yakubu Yaura
Mazauna garin Zaria da ke jihar Kaduna sun shiga cikin makoki bayan samun labarin wata yarinya mai suna Asma’u ‘yar shekara takwas da aka yi garkuwa da ita kuma aka kashe ta bayan kwashe kwana 40 a hannun su.
An zargi wani Kabir, makwabcin mahaifin Asmau, Alhaji Shuaibu Wa’alamu ne ya aikata laifin.
Wani rubutu da wani Musa Ahmed ya wallafa a shafinsa na Hausa Fulani a Instagram ya nuna cewa an sace yarinyar ne a lokacin da take kan hanyarta na sayen katin waya.
Sanarwar ta ce an nemi kudin fansa Naira miliyan 3 ne kuma dangin suka biya amma daga baya wanda ya sace yarinyar ya kashe ta.
“An sace ‘yar abokina, wata yarinya ‘yar shekara 8 a hanyarta ta sayen katin waya a unguwarmu.
“Kwanaki 42 da suka gabata ta kasance tare da wadanda suka sace ta wanda suka bukaci a ba su kudin fansa naira miliyan 3m, amma cikin bakin ciki suka kashe yarinyar daga karshe.
“An ce, watakila yarinyar ta gane wanda ya saceta ne, wanda yake zaune kusa da gidansu, a gaskiya, kusan kullun tana wasa da yaransa.
“Sun kira mahaifinta jiya suna nema
karin kudin da ya wajabta ya aika dashi.
“A yayin da yake jiransu, mutumin ya fusata sosai saboda yana yin sanyin dare, ya kira mahaifinsa ya shaida masa cewa bai ga kowa ba tukuna. Sai mahaifin ya kira lambar ya ce su fada masa gaskiya idan sun kashe yarinyar.
“Sai suka ce, sun kashe ta, tare da binne ta a cikin wani ƙaramin kabari, kwanaki 4 da suka wuce.
“Don takaita labarin, an kama wanda ake zargin da danginsa a daren jiya.” a cewar Musa.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna,ASP Muhammed Jalige, ya ci tura saboda bai dauki waya don tabbatar da hakan ba.