By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bukaci kwamishinan ‘yan sandan jihar da su hada kai da sauran hukumomin tsaro da shugabannin kananan hukumomin da sarakunan gargajiya domin kamo duk wadanda ke da hannu wajen hada-hadar sana’o’in hannu ba bisa ka’ida ba domin gurfanar da su gaban kuliya.
Gwamnan ya zargi wadanda ke aikata haramtattun sana’oin da laifin gurbatar muhalli da ke barazana ga lafiyar mazauna jihar.
Sannan ya ba da umarnin shirya liyafar cin abincin dare da karramawar na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas wanda aka gudanar a ofishin ‘yan sanda da ke Fatakwal ranar Juma’a.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri ya raba wa manema labarai.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Cif Emeka Woke, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar shawo kan masu satar danyen mai da tace shi baki daya.
Wike ya bayyana cewa gwamnati a shirye ta ke ta baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro duk abin da ake bukata domin wargazawa tare da kawo karshen ayyukan matatun mai a jihar Ribas.
A cewar sa, “Jihar ta shirya tsaf domin yakar su fiye da kowane lokaci.”
Gwamnan ya ce tun lokacin da kwamishinan ‘yan sanda, Friday Eboka ya hau kan karagar mulki a shekarar da ta gabata jihar Ribas ta samu zaman lafiya da kuma inganta aikin ‘yan sanda.
“Ba abin mamaki ba ne alkaluman laifuka a jihar ya ragu sosai. Mun dauka mu ne kawai muke shaidawa, amma da kyautar da ka samu daga matar Sufeto Janar na ‘yan sanda, wannan sheda ce ta gaske cewa abin da muke gani a jiha shi ma daga dukkan al’ummar kasa ake lura da shi,” inji Wike. ya bayyana.
Gwamnan ya ce aikin ‘yan sanda a jihar Ribas ya samu kyautatuwa saboda yadda jami’an ‘yan sandan Najeriya a hedikwatar rundunar na jihar suka nesanta kansu da harkokin siyasa.
“A matsayinmu na Jiha, za mu ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro a Jihar. Taimakon da muke baiwa hukumomin tsaro bai dogara da rundunar ‘yan sanda kadai ba. Haka nan muna mika irin wannan karimcin ga sojojin ruwa, sojojin sama da sauran su. A gare mu, mun yi imanin babban aikin kowace gwamnati mai alhakin shi ne kare rayuka da dukiyoyi. Don haka ba mu da wani zabi da ya wuce mu ci gaba da ba da goyon baya wajen samar da kayan aiki da duk wani abu da zai sa hukumomin tsaro su yi aiki sosai a jihar.
Sannan Gwamnan ya sanar da bayar da tukuicin Naira miliyan daya ga kowane daya daga cikin wadanda suka samu lambar yabo ta rundunar ‘yan sandan jihar Ribas da kuma naira miliyan 10m ga hukumar da ta shirya taron.
Eboka ya bayyana cewa shekarar 2021 shekara ce mai ban mamaki domin jihar Ribas ta zama daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.