Kamfanin layin waya na Airtel na Nijeriya ya bayyana cewa zai kashe naira miliyan 300 a matsayin gudummawarsa wajen yaki da cutar annobar korona. Airtel ya ce zai kashe wannan kudin ne a matsayin daya daga cikin ayyukan da za su yi a daidai lokacin da suke murnar cika shekara 10 suna kasuwancinsu a Nijeriya.
Babban Manajan Daraktan Kamfanin, Segun Ogunsanya ya kara da cewa sun ware naira miliyan a matsayin kashin karshe cikin naira biliyan 1.9 da kamfanin ta yi alkawari cikin watan Afrilu cewa za ta kashe kan annobar na Korona.
Ogunsanya ya tabbatar da hakan ne a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce za su yi amfani da wannan damar wajen mika godiyarsu da farin cikinsu ga ‘yan Nijeriya bisa gudummawa da goyon bayan da suke ba su.