By Abbas Yakubu Yaura
Kamfanin Air Peace Limited a ranar Asabar ya ce nan ba da jima wa ba zai dawo da zirga-zirgar jiragensa zuwa Dubai.
Sanarwar, wacce aka sanya a shafin kamfanin na Instagram ta bayyana cewa kamfanin zai ci gaba da hidimar sa na jigilar Fasinjoji zuwa Dubai a makonni masu zuwa.
Kazalika sanarwar mai taken “Sabon Labari Daga Kamfanin Air Peace, zai fara harkokinshi zuwa Dubai”, inda Kuma Kamfanin ya ce, zai yi Karin bayani game da zirga-zirgansa.
Sanarwar tace, “Air Peace na farin cikin sanar da abokan Huldasa cewa zai ci gaba da jigilan fasinjoji zuwa Dubai ta Sharjah a cikin makonni masu zuwa.
“Wannan ya biyo bayan matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na dage Takunkumin zirga-zirgar jiragen saman Kamfanin zuwa Daular Larabawa wato UAE.
“Za a Kuma ayi ƙarin bayani lokaci zuwa lokaci, a dukkannin kafofin watsala labaranmu a hukumance.”inji sanarwar.