Wani fada da ya barke tsakanin wasu gungun ‘yan bindiga biyu a jihar Katsina, ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin shugabanninsu da kuma wasu mutum uku.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe shugaban yan bindiga ne Mai suna Dogo Nabajallah, a cikin dajin Dungun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar, a ranar Larabar da ta gabata, bayan wasu mambobin daga wata kungiyar yan ta’addan da ke hamayya da wacce na Nabajallah ke jagoranta, sun yi mishi duran mikiya, kan batutuwan da su ka shafi auren wata Mace.
Wasu mazauna yankunan da ke makwabtaka da su, wadanda su ka bukaci a sakaye sunayen su sun ce, musabbabin harin shi ne, mambobin kungiyar masu hamayya da juna, ba su ji dadin yadda Nabajallah ya tsoma bakin shi ba, a cikin lamarin auren,
Kazalika wasu rahotannin kuma na nuna cewar, mambobin kungiyar Nabajallah, wadanda mutuwar shi ta firgita su, sun yi bata kashi da mambobin kungiyar hamayyar, yayin da su ka kashe Mutum uku daga cikinsu.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC ba ta da Dan takara a zaben Gwamnan jihar Anambra, inji Peter
Wani mazaunin yankin a jiya Alhamis ya bayyana cewa, “Tun da aka kashe Nabajallah a jiya ranar laraba, mu na taka-tsan-tsan yayin zuwa kusa da dajin don yin noma. Wasu daga cikin mu ma, sun yanke shawarar dai-na zuwa can, don yin noma, har sai tashin hankalin ya lafa a tsakanin yan bindigan ” Inji shi.
Kazalika ana yautata zaran cewa, magoya bayan Nabajallah tuni suka birne gawar shi a cikin dajin, tun a ranar Laraba.
A nashi bangaren Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, har izuwa hada wannan rahoton, bai ce komai ba kan wannan lamarin.