Wani Matashi a Jihar Adamawa ya caka wa abokin shi wuka inda ya aika shi lahira bisa zargin shi da sace Mishi wayar salula ta dubu hamsin da biyar, kamar yadda jami’an yan sanda suka tabbatar.
Matashin Mai suna Abdulkareem dan kimanin shekara goma sha takwas, ya shiga komar yan sanda ne bayan da ya yi wannan aika-aika kan abokinsa mai suna Ayuba a garin Mubi na Jihar ta Adamawa.
Wanda ake zargi da wannan katobara wato Abdulkareem, ya shaida wa manema labarai cewa sun koma gida barci shi sa wasu abokan shi biyu bayan da hakarsu ta sace Jarkar Mai a wani gidan mai ta gaza cimma ruwa.
Ya ce to bayan farkawar shi cikin dare ne ya tarar da cewa sai dai gurin zaman wayar, amma ita kam babu labarin ta, kuma bai yi wata-wata ba ya garzaya gurin abokan nashi da sanyin safiya don labarta musu wannan al’amari, inda su kuma suka tabbatar Mishi da cewa Ayuba ne Kadai ya shiga dakin bayan tafiyarsu.
Sai dai al’amarin ka da shedan, bayan da ya tunkaru Ayuba da zance nan fa hayaniya ta kaurw har ta kai ga abokan nasu sun bada shawarar zuwa bakin wani rafi don raba raini.
Amma gabannin isar su rafin ne a cewar Abdulkareem kawai ba tare da ya aune ba ya ji saukar dutse a kan shi wanda Ayuba ya dake shi da shi, inda shi kuwa ba tare da kai zuciya nesa ba, ya zaro wuka ya daɓa mishi a hannu da kuma Kirji inda nan take ya ce ga garin ku.
Kakakin Rundunar Yan sandar Jihar DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da cewa wanda zargi dole ya girbe abinda ya shuka da zarar an kammala bincike.