Akalla kananan hukumomi 47 a shiyyar Arewa maso Yamma ne ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ke ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Daily Post ta ruwaito cewa, Bincike ya nuna cewa galibin kananan hukumomin na fama da hare-haren ta’addanci a kullum daga ‘yan bindigar yayin da suke gudanar da ayyukansu ba tare da wani kalubalantar gwamnati ba, saboda babu wata alamar wanzuwar hukumomi.
‘Yan bindiga a wasu jihohi kamar Zamfara, Sokoto da Katsina na sanya haraji a wasu yankuna a kan mazauna yankin domin ba wa jama’ar yankin kariya daga gungun ‘yan daba masu adawa da juna.
Jihohin Katsina da Sokoto da Zamfara da ke da kananan hukumominsu a kan iyakar Najeriya sun dogara ne da jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da su domin kare lafiyar al’ummar yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yaɗuwar Makamai, Laifin Hukumar Kwastam Ne, Da Hukumar Kula Da Shige Da Fice—- CISLAC
Karamar hukumar da ta fi fama da ta’addanci a shiyyar arewa maso yamma sun hada da 18 a Katsina, 11 a Sokoto, Zamfara 10 da Kaduna 8.
A jihar Katsina, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Batsari, Safana, Jibia, Danmusa, Sabuwa, Kankara, Dandume, Faskari, Dutsinma, Kurfi, Batagarawa, Rimi, Danja, Kafur, Matazu, Kankia, Malumfashi da Katsina.
A jihar Kaduna kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Chikun, Kajuru, Kachia, Zangon Kataf, Kauru, Lere, Birnin Gwari da Giwa.
A jihar Zamfara, kananan hukumomi goma da ‘yan fashi ke ci gaba da addabarsu sun hada da Bakura, Birinin Magaji, Maru, Tsafe, Anka, Maradun, Shinkafi, Bukkuyum Zurmi da kuma kananan hukumomin Gusau wadanda tun daga lokacin hare-haren ‘yan bindiga ya fara shafansu a jihar.
Bayanai sun nuna cewa a jihar Sokoto, yankunan da rikicin ya shafa sun hada da Illela, Rabah, Sabon Birni, Isa, Wurno, Gada, Goronyo, Tangaza, Gudu, Dange Shuni da Kebbe.
Al’ummar wadannan kananan hukumomin da ke yankin Arewa maso Yamma sun ce sun bar yankunansu tare da iyalansu domin tsira da rayukansu yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar yankunan su.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa tun bayan yawaitan hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma musamman jihar Zamfara, daukacin tsarin Almajeri ya tabarbare yayin da talauci ke kara kamari a tsakanin al’umma, tare da samun yawaitar Marayu da Zaurawa.
Wasu daga cikin wadannan Zaurawa da marayu da suka zanta da Majiyar Dimokuradiyya sun ce duk da cewa an ba su sansanoni a matsayin ‘yan gudun hijira, gwamnatin jihar ba ta ba su abinci ba don haka ne suka fito suna yawo kan tituna domin neman sadaka.