Ana ci gaba da samun tsaikon tafiye-tafiye a sassa daban-daban na kasar Jamus, sakamakon saukowar dusar kankara mai yawa da ma iska mai karfi da ke kadawa.
Hukumomi sun ce matsalar za ta kai akalla wasu kwanaki nan gaba, abin da zai ci gaba da shafar tafiye-tafiyen da matafiya suka tsara musamman ta jiragen kasa.
Kamfanin jiragen kasa na Jamus, Deutsche Bahn, ya sanar da soke tafiye-tafiyen da dama a karshen mako masalan masu dogon zango.
Su ma jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin datse hanyoyin motoci da dama inda aka lura da santsin da dusar kankarar ke haddasawa da kuma ke iya janyo hadura a kan hanyoyin.
Hukumomi na shawartar mutane da su soke tafiye-tafiyen da ba su wajaba ba, musamman a kawanakin farko na wannan mako.