By Abbas Yakubu Yaura
Sakamakon rikicin hada-hada da ya addabi masana’antar shirya fina-finan Kannywood a Kano, fitaccen jarumi kuma mawaki Naziru Sarkin Waka ya baiwa Ladin Cima kyautar Naira miliyan biyu domin ta fara kasuwanci da magance wasu matsalolinta na rayuwa.
Naziru Sarkin Waka ya bayyana hakan ne a wani tabbataccen sakon da ya wallafa a shafin sa na Facebook.
A makon da ya gabata Ladin Cima wata tsohuwar jaruma ce a Kano tun ma kafin a fara fitowa a Kannywood ta shaida wa sashen Hausa na BBC cewa nan ba da dadewa ba za ta iya shiga cikin wadanda basu da muhalli a Kano kasancewar masana’antar shirya fina-finan Kannywood bata ba ta wani abu daya wuce Naira dubu biyu a lokacin da ta fito a kowane fim ba.
Wannan ikirari nata ya janyo cece-kuce a masana’antar Kannywood inda wasu suka goyi bayan da’awar ta Ladin Cima.
A wata karkatacciyar hanya Naziru Sarkin Waka ya marawa Ladin Cima baya inda ya tabbatar wa duniya cewa ta fadi gaskiya.
A cewar Naziru ba wai Ladin Cima ba da yawa daga cikin jaruman Kannywood har suna fitowa a fina-finan kyauta ba tare da an biya su Kobo ba.