Dan takarar gwamnan na Jamiyyar NNPP Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar lashe karamar hukumar Rano, daya daga cikin kananan hukumomin jihar Kano 44.
Baturen zaben karamar hukumar Farfesa Adamu Jibril Alhassan na jami’ar Bayero Kano, shine ya tabbatar da nasarar jamiyyar, inda ta samu kuri’u 18040.
KU KARANTA: INEC Ta Daga Zabukan Wasu Kananan Hukumomin Jihar Rivers
Sai kuma jamiyyar APC wadda tazo ta biyu da kuri’u dubu 17 a zaben na jiya da aka gudanar.
Har yanzu dai ana ci gaba da tattara sakamakon zabe na gwamna da yanzu haka hukumar INEC ke yi, tare da wallafa sakamakon kai tsaye a shafin data samar na IRev.
Kawo yanzu dai hukumar INEC ta wallafa sakamakon zaben na jihar Kano , 6,826 wanda hakan ke daukar Kaso 60.83 na adadin kuri’un da aka kada ke nan.
A wani labarin kuma: INEC Ta Sanya Sakamakon Zabe 66,634 Zuwa Dandalinta Na IReV
Ya zuwa yanzu dai hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta tura sakamakon zabe 66,634 na zaben gwamnoni da na majalisun jihohi a dandalinta na IReV.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa jam’iyyun adawa da wasu ‘yan Najeriya sun caccaki INEC kan gazawarta na sanya sakamakon nan take a dandalinta na kallon sakamakon zabe IReV da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.