By Ishaq Dabai
An samu daidaito tsakanin kungiyar manoma da Yan kwangila tare da hukumar Raya kogunan Hadeja Jama’are, wajen rufe dam din Tiga. Tsawon watanni biyar tare da gudanar da muhimman ayyuka don inganta ayyukan noma a arewancin kasar nan.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban hukumar Raya kogunan Hadeja Jama’are Alhaji Ma’amun Da’u Aliyu, lokacin daya jagorancin zaman kwamitin hukumar dake nan Kano.
Daya yake nasa jawabin a madadi Manoman, Mustafa Adamu Mudawa sakataren kungiyar manoman Rani ta kasa reshen jihar Kano, ya ce da yardar Manoman ranin aka cimma wannan matsaya na rufe ruwan. Domin yashe manya da kananan madatsun ruwa.
Kazakika wanda ya tsara taswirar Kuma mataimakin Mai duba yadda aikin ke gudana a kananan hukumomin kura da Garum Malam da Kuma Bunkure Engr. Sabi’u Dan Malam ya bada tabbacin kammala aikin a wa’adin da kwamitin ya cimma matsaya.
Daga karshe yayi kira ga Al’ummar yankin dasu bada hadin Kai don ganin an kammala wannan aiki cikin Nasara.
Comments 1