By Abbas Yakubu Yaura
Wasu Dalibai biyar daga jihar Kano sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina a ranar Alhamis.
Daliban daga kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi Kano, an ce suna kan hanyarsu ta zuwa Katsina ne domin halartar bikin kaddamar da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) lokacin da tayar motar tasu tafice inda hakan yasa motar ta yi hatsari.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wani da hatsarin ya rutsa dashi Abdullahi Muhammad yace yanzu haka suna babban asibintin garin Bichi inda ake neman jini dan sanyawa wadan abin ya rutsa da su.
Kokarin samun ainihin wurin da sauran bayanai na faruwar hatsarin bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto domin kwamandan hukumar FRSC reshen Kano Mato Zubairu bai amsa sakon da muka aike ba lokacin da aka tuntube shi.
A halin da ake ciki kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta bada umarnin gudanar da zaman makoki na kwanaki 3 kan rasuwar daliban.Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mikail Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na shiyyar (A).
Comments 2