By Ishaq Dabai
Gobara ta tashi a gidan Rediyo da Talabijin mallakar Gwamnatin Jihar Kano ARTV dake unguwar Hotoro a yammacin ranar Juma’a.
Babbar Daraktan tashar, Hajiya Sa’a Ibrahim ta tabbatar faruwar lamarin a cikin wata hira da tayi da manema labarai.Sa’a Ibrahim tace injiniyoyi ne suka sanar da ita tashin gobarar kuma nan take suka shiga aikin kashe ta gadan gadan.
Wata majiya ta shaidawa Jaridar Solacebase cewa barkewar gobarar ta lalata daya daga cikin dakin yada shirye shirye dake gidan talabijin din.
Tace matasan da ke buga kwallon kafa a filin tashar sun ba mu taimako kafin isowar jami’an kashe gobara.
Sa’a Ibrahim wanda kuma ita ce Shugaban Kungiyar Watsa Labarai ta Najeriya (BON) tace an sanar da Kwamishinonin Ayyuka da Bayanai kan barkewar Gobarar.