Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, a karkashin sashin kula da zirga-zirgar ababen hawa (MTD), ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 391 daga hadurran mota 275 da suka auku daga watan Janairu zuwa Watan Disambar shekarar 2021..
Har ila yau, a shekarar 2021, rundunar ta ce mutane 522 ne suka jikkata tare da yin asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira a sakamakon hadurran mota a fadin jihar.
Babban Jami’in dake kula da sashin na MTD a jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya ne ya bayyana hakan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a babban Ofishin sashin kula da zirga-zirgar ababen hawa dake jihar.
Comments 1