By Ishaq Dabai
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran laifuka masu alaka da haka ICPC tace ta kwato motar aikin mazabar da ake zargin karkatar da ita zuwa amfani da dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Nasarawa, a jihar Kano.
Babban Mataimakin Sufeto Janar na ofishin ICPC na Kano, Bukar Galadima ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata bayan da jami’an tsaro suka bi diddigin motar aikin mazabar da aka boye a wani wuri a cikin birnin. .
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa shugaban tawagar sa ido kan ayyukan mazabu na ICPC ya ce sun gano cewa dan majalisar da ke wakiltar mazabar Nasarawa a majalissar tarayya ne ya dauki nauyin motar da sunan ayyukan mazabu don amfanin al’ummarsa amma an gano cewa an canza batun zuwa amfanin kansa, Ya ce hukumar ta kwace motar don ci gaba da bincike.
Ya kara da cewa,”Mun gano cewa an saki kudi kimanin Naira miliyan 13 don siyan motar kirar Ford 2019 inda aka fitar a cikin kasafin kudin motar aikin mazabu, ” in ji shi.
Galadima yace hukumar za ta gurfanar da dan kwangilar da mai daukar nauyin aikin da a karkatar da zaran an kammala bincike, Idan za’a iya tunawa kwanan nan jaridar Solacebase ta rawaito cewa ICPC ta binciki wasu ayyukan mazabu a Kano, a wasu kananan hukumomin da suka hada da, Kiru, Bebeji, Warawa, Dawakin Kudu, Tarauni, Kano Municipal, da Dala, Sauran sune Dawakin Tofa, Dambatta, Bichi da Nasarawa don tabbatar da cewa an aiwatar da asusun da aka ware kamar yadda doka ta tanada.