By Ishaq Dabai
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da Sauran laifuka ICPC tace zata gurfanar da ‘yan kwangilar suka gaza gudar da ginin makarantun mazabu a jihar kano.
Babban mataimakin shugaban hukumar ta ICPC na jihar kano Bukar Galadima shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar a sabar a yayin gudanar da duba yadda aikin ginin makarantun yake tafiya a firamare Zogarawa dake karamar hukumar Dawakin kudu, wanda sanata mai wakiltar kano ta tsakiya ya dauki nauyi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa shugaban hukumar Galadima yace mafiya yawan daga cikin makarantun da ake ginawa sanata mai wakiltar kano ta tsakiya ne yake bada aikin kwangilar amma duk mun same su da lahani wanda kuma ba’a gudanar dasu bisa ka’idar kwangilar ba.
Mun gurfanar da dukkanin ‘yan kwangilar nan take sai mungama kammala bincike,” a cewar Galadima.
“Dukkanin aikin gina makarantun firamare da suke karkashin mazabar an ginasu tun a shekarar 2020 inda akayi aiki marar inganci mafiya yawan daga cikin rufin makarantun yayyo yakeyi tare da fantin da akayi musu bashi inganci da kujeru.
Ya kara da cewa zamu cigaba da bin sauran ayyukan da suke karkashin mazabun na jihar kano a wasu daga cikin kananan hukumomin Warawa, Dawakin Kudu, Tarauni Kano Municipal, da kuma Dala.
Kazalika yace suna bibiyar aikace aikacen a cikin kasar nan inda ake kashe makudan biliyoyin kudade tundaga shekarar 2000 batare da aiki mai inganci ba.