Rundunar ‘yan sandan farin kaya (DSS) reshen jihar Kano, ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan wata kungiyar asiri ne da suka kware wajen bin diddigin mutane a bankuna domin su yi musu fashi bayan fitar da kudi a bankunan.
Daraktan Hukumar ta DSS na jihar, Alhassan Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano yau Juma’a, inda ya kara da cewa masu laifin sun shafe shekaru uku suna ta’addancin ga al’ummar jihar.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da suka haɗar da Abubakar Umar, 30, Abubakar Suleiman, 38, da Ya’u Abubakar, 35.
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne bayan sun kwace babur tare da yi wa mai shi fashin kudi naira 300,000, bayan wanda abin ya shafa ya ciro Kudin daga bankin.
Muhammad ya ce tuni hukumar ta ajiye jami’anta domin tabbatar da kama sauran ‘yan kungiyar.