By Ishaq Dabai
Jami’an ‘yan sanda a jihar Kano a ranar Talata sun ce sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi masu samar da man fetur ne ga mahara a jihar Katsina dake makwabtaka da jihar.
Mutum biyun da aka kama sun hadar da, Jamilu Abdullahi, direban motar, J5 mai dakon kayan sai dayan kuma, mai suna Musbahu Rabi’u.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da kamen, yace an kama wadanda ake zargin ne bisa ga bayanan sirri yayin da suke jigilar kayan man fetur da aka boye cikin buhunan sukari zuwa ga mahara a yankin Jibia na jihar Katsina.
DSP Haruna yace, “A ranar 15/10/2021 da misalin karfe 1230, tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Abubakar Hamma yayin da suke aikin sintiri a karamar hukumar Fagge, jihar Kano sun tare Motoci J5 guda biyu (2) dauke da kayan abinci, A shingen bincike, an gano jarkoki guda biyar (5) masu daukar lita 25 kowannensu cike da man fetur da aka ɓoye a cikin buhu na sukari babu komai daga ɗayan motocin.
“kazalika, an kama mutum biyu da ake zargi, Musbahu Rabi’u, dan shekara 31, na Karamar Hukumar Jibiya, Jihar Katsina da direban motar J5, Jamilu Abdullahi, dan shekara 37 shima a Jibiya, Jihar Katsina.
“A binciken farko, Jamilu ya furta cewa, ya taba zuwa Kano daga Katsina ya sayi man fetur a cikin Jarkoki dan ya dauka ya kai Jibiya, Jihar Katsina inda ya sayar da shi da tsada.Ya kuma yi ikirarin cewa, an damke shi ne yayin da yake kokarin jigilar man fetur a karo na biyu.
“Kwamishinan ‘yan sandan, reshen jihar Kano ya ba da umurnin a gudanar da bincike na gaskiya, bayan haka za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bukaci mutanen kirki na jihar dasu kasance masu sanin yakamata da lura da muhallin su na kusa wajen kai rahoton duk wani tuhuma da faruwar hakan ga ofishin‘ yan sanda mafi kusa. Ya kuma yi kira ga Ma’aikatan Gidan Man Fetur a jihar dasu guji siyar da man fetur ga masu siye da ba a san su ba da yawa a cikin Jarkoki kuma su kai rahoton duk wani mai siye da ake zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.