Daga: Ibrahim Hassan Hausawa
Wani jami’in gidan gyaran hali na Goron Dutse da ke Kano wanda har yanzu ba a tantance ba ya kashe wani dan kasuwa da ya ki sayar masa da taba sigari.
Shaidun gani da ido sun shaida wa JARIDAR DIMOKURADIYYA cewa an samu rashin fahimtar juna a tsakanin mutanen biyun bayan dan kasuwar ya ki sayar wa jami’in taba sigari.
“Ba za mu iya cewa da gaske ba, amma, da alama jami’in yana bin dan kasuwar ne kuma a wannan karon, ya ki sayar masa da taba sigarin wanda hakan ya jawo martaninsa yayin da ya harbe shi kwatsam babu zato,” in ji wani ganau.
An tattaro cewa harsashin da aka harbi dan kasuwar ya ratsa ta cikinsa ya taba wani mutum a kafarsa dake kusa dashi.
Daga nan ne aka garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Sai dai Kiyawa ya ce ‘yan sandan na ci gaba da kokarin gano ko wane ne dan kasuwar da aka kashe.
Da aka tuntubi mai magana da yawun gidan gyaran hali na jihar Musbahu K/Nasarawa, ya ce zai dawo ga wakilinmu.