Jam’iyyar NNPP ta fitar da sunayen yan takarar da take fatan su tsaya mata a zaben 2023, dake tafe.
A wata Sanarwa da jam’iyyar ta rabawa manema labarai a daren Jiya, ta bayyana Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan ta, da kuma Comrade Aminu Abdussalam a matsayin mataimakin Gwamna.
Dangane da sanatoci Kano Guda Uku kuwa, yanzu haka Jam’iyyar ta zabi Sanata Ibrahim Shekarau a Matsayin Dan Takarar Kano tsakiya, sai Abdurrahman Kawu Sumaila Dan Takarar Sanatan Kano ta Kudu, da kuma Dr. Abdullahi Baffa Bichi a matsayin dan takarar jam’iyyar NNPP a sanatoriya ta Arewa.
Kazalika kunshin sanarwar ya kuma bayyana sunayen yan takarar majalisar wakilai ta tarayya da jihohi a daukacin kananan hukumomin Kano 44.
A karamar hukumar Gwale jam’iyyar ta tsayar da Garba Diso, da kuma Abdulmajid Isa a matsayin tarayya da jiha.
Abun mamakin shine babu sunan Babangida Yusuf Dawo Dawo wanda shine ɗan majalisar jiha mai ci a karamar hukumar Gwale, kuma ya koma NNPP a kwanan nan.
Kazalika sauran kananan hukumomin suma jam’iyyar ta bayyana sunayen mutane daban daban wadanda zasu tsaya mata takarar a zaben 2023.
Dala
Hon. Aliyu Sani Madaki
Hon. Lawan Hussain
Bichi
Hon. Ahmad Garba Bichi
Hon. Hamza
Kano Municipal
Sagir koki
Sarki Aliyu Daneji.
Bunkure /Rano/Kibiya
Hon. Kabiru Alhassan Rurum
Hafizu Gambo Gurjiya
Shehu Fammar
Tsanyawa /kunchi.
Yusuf Ali Muhammad
Tarauni
Muntari Yarima
Kabiru Dahiru Sule
Fagge
MB Shehu
Tukur Muhammad
Rogo
Malam Abdullahi Rogo
Jibril falgore
Bagwai/ Shanono
Barr. Nura Abdullahi
Hon.
Bebeji
Abdulmumin Kofa.
Ali Tiga
Tudun Wada /Doguwa
Yushau Abdullahi Soja.
Abdullahi Yaryasa
Danbatta / Makoda
Hon. Badamasi Ayuba
Hafizu sani maidaji
Nasarawa
Umar Tanko Yakasai.
Yusuf Bello Aliyu
Ajingi
Tini Lawan
Minjibir /Ungoggo
Sani wakili
Aminu Saadu
AA. Minjibir
Kura/ Madobi /Garun Malam
Shehu Naallah Kura
Zubairu Mahmud Madobi
Abdulmalik Juda
Kumbotso
Hon. Idris Dan Kawu
Hon. Mudasssir Ibrahim Panshekara
Takai
Hamza Safiyanu.
Warawa
Shehu Alhai Abdulkadir
1504026116. 07026820445