Babbar kotun Tarayya Dake zamanta a jihar Kano ta Bayyana Shehu Wada Sagagi a matsayin Wanda zai Cigaba da zama shugaban Jam’iyyar PDP na Kano.
Cikin Wani Hukunci da Ya Bayar Alkalin Babbar Kotun Mai shari’a Liman yace Shehu Wada Sagagi zai Cigaba da Kasancewa shugaban Jam’iyyar har lokacin da zai Yanke Hukunci.
A Ranar 17 ga watan Nan da Muke ciki ne Mai shari’a Am Liman ya Bayar da Wani Hukunci da Ya Dakatar da shehu wada sagagi da Bayyana Kansa amatsayin shugaban Jam’iyyar ta PDP.
Sai Dai Kuma a zaman kotun na yau Mai shari’a Am Liman ya Bayyana cewa Shehu Wada Sagagi ya Cigaba da jagorantar jam’iyyar saboda Gaza Kawo kwararan Hujjoji akan zarge zargen da akeyi masa.
Wani Mai suna Bello Bichi shine ya shigar Da Kara Yana Zargin Shehu Sagagi da yiwa PDP zagon kasa Yana Mai cewa Sagagi yaron Kwankwaso ne Wanda tuni ya fice Daga Jam’iyyar ta Pdp zuwa NNPP.
Mai shari’a ya ɗage shari’ar Zuwa Ranar 26 ga watan nan da Muke Ciki.