By Ishaq Dabai
Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Talata ta yanke wa wani mai suna Aminu Inuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe matarsa Safara’u Mamman, da wuka har lahira.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Inuwa, mazaunin unguwar Gwazaye ne dake Dorayi Babba Kano kotun ta same shi da laifin kisan.
Alkalin dake gudanar da shari’ar, Mai shari’a Usman Na’abba, yace lauyan masu gabatar da kara ya tabbatar da shari’arsa ba tare da shakka ba, don haka ya yanke wa mai laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Lamido Sorondinki, ya sanar da kotun cewa mai laifin ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Afrilu na shekarar 2019 a unguwar Gwazaye dake Dorayi Babba ta jihar Kano.Sorondinki ya kara da cewa a ranar ne da misalin karfe 12:00 na rana wanda ake kara ya samu rashin jituwa tsakanin sa da matarsa Safara’u Mamman.
Bayan samun rashin jituwar ne “Ana cikin haka sai wanda ake kara ya yanke mata makogwaro da wukar dafa abinci mai kaifi har ta mutu sannan ya binne ta a wani daki da ba a kammala ba a gidan sa dake Dorayi Babba ta Kano”
Lauyan masu gabatar da kara ya gabatar da shaidu uku don tabbatar da tuhumar sa.Sai dai wanda aka yankewa hukuncin ya musanta zargin aikata laifin.
Lauyan dake kare wanda ake kara, Barista Mustafa Idris, ya gabatar da shaida guda daya ga kotun don kare wanda yake karewa.