Kungiyar Ma’aikatan kananan hukumomi ta jihar Kano, NULGE, ta bukaci sabon gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya kungiyar a sahun gaba, domin aiki tare wajen aiwatar da kudurorin da ya tanada ga ƙananan hukumomin jihar nan.
Shugaban Kungiyar na jiha Kwamared Abdullahi Muhammad Gwarzo, Matawallen Gwarzo ne ya bukaci hakan, ta cikin wata takardar sanarwar manema labarai daya aikewa da manema labarai, a Kano, da yammacin Asabar din nan, mai dauke da sa hannunsa.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Real Madrid Ta Soke Kwantiragin Eden Hazard
Kwamared Gwarzo ya tabbatarwa da Gwamnan cewa a shirye kungiyar su take, domin tallafa masa wajen gudanar da aikin da yake fata, domin ci gaban kananan hukumomin Kano da Ma’aikatan baki daya.
Daga nan sai shugaban kungiyar ya yabawa daukacin ma’aikatan kananan Hukumomi na jiha, tare da bukatar su Rubanya kokarin da suke a yayin gudanar da ayyukan su.
Daga nan sai shugabancin kungiyar ya taya sabon zaɓaɓɓen gwamnan Injiniya Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa murna shiga Ofis domin fara gudanar da Mulki.
A wani labarin kuma: Kungiyar Gwamnonin PDP ta Samu Sabon Shugaba
Jam’iyyar PDP ta zabi gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin jamiyyar na kasa.
Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri ne ya sanar da hakan a karshen wani taron sirri da gwamnonin suka gudanar a ofishin gwamnan jihar Bauchi a ranar Asabar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa gwamnonin jam’iyyar PDP, da yan kwamitin gudanarwarta na kasa, da masu ruwa da tsaki sun hallara a dakin taro na Banquet da ke fadar gwamnatin jihar Bauchi.