By Abbas Yakubu Yaura
Masarautar Gaya ta tunbuke rawanin Dagacin kauyen Gudduba Mallam Usman Muhd Lawan nan take dake karamar hukumar Ajingi a jihar Kano.
DUBA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Tafi Zuwa Malabo Domin Halartar Babban Taron AU
Maimartaba Sarkin Gaya Dr Aliyu Ibrahim Abdulkadir ne ya bada umarnin cire dagacin a ranar Laraba bayan yayi umarnin gudanar da cikakken bincike kan laifukan da ake tuhumar dagacin inda aka gano yana da hannu dumu dumu wajen aikata laifukan kwace filayen jama’ar da yake mulka.
Dakta Aliyu ya umarci Madakin Gaya Hakimin Ajingi daya gabatar da sunayen wadanda suka cancanta don maye gurbin dagachin nan bada jimawaba.
Sarkin na Gaya ya kuma nanata cewa masarautar Gaya bazata kyale duk wanda aka kama da rashin tarbiyya ko kuma wasu halaye da zasu bata kyakkyawan su nan masarautar ba, ya kuma ja hankalin Hakiman da Dagatan masarautar da masu rike da mukamai dasu yi jagoranci bisa gaskiya da rikon amana.
Idan dai za’a iya tunawa a ranar 9 ga watan Maris Majalisar masarautar Gaya ta dakatar da Dagacin kauyen Gudduba Mallam Usman Muhd lawan da ke karamar hukumar Ajingi, inda nan take umarnin ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sarki Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir shine ya sanar da hakan, inda ya ce ana zargin Dagacin kauyen ne da hannu dumu dumu wajen kwace filayen mutanen da yake mulka.
Sannan sarkin ya umarci Dagacin da ya mayarwa da wadanda duk suke da ikon mallakar filayen da ya kwace.
Kazalika an umarci tubabben Dagacin da ya gurfana a gaban Masarautar domin amsa tambayoyi.
Comments 1