By Isahq Dabai
An bukaci al’ummar da suke karkashin Masarautar Gaya, da su baiwa jami’an hukumar INEC hadin kai yayin gudanar da aikin yin rijistar zabe ta bana da ake gudanarwa ta Internet.
Hakimin Gaya wanda shine Wamban Gaya Alhaji Mansur Ibrahim shine yayi wannan kira azantawar sa da manema labarai a fadar masarautar.
Alhaji Mansur Ibrahim yace rijistar tana da matukar muhimmanci ga kowanne dan kasa dan zabar shuwagabanni na gari a kasa.
Hakimin ya kuma bukaci ma’aikatan hukumar INEC da suyi aiki tare da shuwagabannin gargajiya, da Dagatai wajen wayar da kan al’umma dangane da yadda aikin yake.
Wamban na gaya ya yi kira ga hukumar INEC da su samar da karin wasu kayayyakin aikin a sauran wuraren dake yakin karkara.