Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya, da magance matsalolin da suka shafi lafiyar kwakwalwa.
Mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin kiwon lafiya, Dakta Fauziyya Idris Buba, ita ce ta bayyana hakan, yayin wani taron wayar da kai na yini daya, tare da shugabannin gidajen dake kula da walwalar jama’a da cibiyoyin gyaran hali na jihar.
KU KARANTA: Dan Wasa Iheanacho Ya Samu Tagomashi A Gasar Premier League
Dakta Fauziyya wadda ita ce shugabar kwamitin kula da lafiyar kwakwalwa a jihar Kano, ta ce an shirya taron ne domin tattaunawa kan yadda za a magance matsalar tabin hankali, da shaye-shayen miyagun kwayoyi a
a cibiyoyin gyaran hali.
Ta kuma yi nuni da cewa, za a bai wa jami’an da ke kula da harkokin kiwon lafiya damar bayyana irin kalubalen da suke fuskanta, inda ita kuma zata shige gaba wajen ganin an samar musu da mafita.
DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa sun bayar da karfi ne kan lamurran da suka shafi lafiyar kwakwalwar yara da manya da ke karkashin kulawar su, da kuma shirya cikakken rahoto domin mikawa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da nufin daukar matakin da ya dace.
Dakta Fauziyya ta bayyana matsalar tabin hankali a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka shafi kiwon lafiya da aka yi watsi da su, domin galibin mutane ba sa ba shi fifiko sosai kuma galibi suna kyamatar wadanda abin ya shafa.
Daukacin wadanda suka halarci taron sun bayyana gamsuwar su, kan yadda suka gabatar da matsalolin da suke.fuskanta kuma Dakta Fauziyya ta bayyana shirin ta na daukar matakin da ya kamata.
kazalika da dama cikin su sun bayyana cewa nasu da matsalar abinci, da kuma magunguna, domin kuwa gwamnati na yin bakin kokarin ta wajen samar musu da komai isasshe.
A wani labarin kuma: FG Na Shirin Kara Albashi Ga Ma’aikatan Ta – Boss Mustapha
Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Boss Mustapha, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kuduri aniyar inganta mafi karancin albashin ma’aikata domin bunkasa aikin da suke.
Boss Mustapha wanda shi ne babban bako na musamman a wajen kaddamar da kotun Hassan Sumonu, ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin.