Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Kano, a ranar Talata ta ce ta kama mutane akalla 85 da ake zargin dillalan miyagun kwayoyi ne a wani kulob a jihar,kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari a wata sanarwa da ya fitar ya ce an kama mutanen ne bayan wani samame da suka kai a wani kulob na Bubles da ke Kano wanda aka ce an mayar da shi wurin hada-hadar maggun kwayoyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Bada Belin Wani Malamin Addini Kan Wasu Tsauraran Sharudai
Ya ce an kai harin ne saboda korafe-korafen da al’umma ke yi game da ayyukan da suka shafi muggan kwayoyi a kulob din.
Maigatari ya ce Kwamandan CN Abubakar Idris Ahmad ya tura jami’ai masu hankali don gudanar da sa ido kan kulob din wanda hakan ya sa aka kama su.
“A yayin farmakin, jami’an hukumar sun samu nasarar cafke maza 55 da mata 30. Wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi yunkurin kaucewa kama su ne ta hanyar tsallake shingen katangar kulob din yayin da wasu kuma suka yi kokarin boyewa a cikin firji.
“Duk da haka, JTF ta yi nasarar kame su duka,” in ji Maigatari.
Ya kara da cewa kama wadanda ake zargin babbar nasara ce ga hukumar NDLEA a yakin da take yi da ayyukan da suka shafi muggan kwayoyi a jihar Kano.
“Hukumar ta dukufa wajen ganin an dakile safarar miyagun kwayoyi da ta’ammali da miyagun kwayoyi, wadanda suka zama babbar matsala a jihar da ma kasa baki daya.
“Yana da mahimmanci a lura cewa shaye-shayen kwayoyi da fataucin miyagun kwayoyi suna da mummunan sakamako, ba kawai ga mutanen da abin ya shafa ba har ma ga al’umma baki daya.”
Ya yi nuni da cewa, wadanda ake zargin suna kan bincike domin gano masu sayar da magunguna a cikin su wadanda ko shakka babu za su fuskanci fushin doka da kuma masu amfani da muggan kwayoyi domin a mika su ga sashin da ya dace domin ba da shawara da kuma shiga tsakani.
Sai dai kakakin rundunar ya fitar da sanarwar gargadi daga kwamandan cewa babu gurin buya ga masu sayar da muggan kwayoyi a jihar, ya kuma bukaci jama’a da su kai rahoto ga hukumar.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Majalisa Dattawa Ta 10 Zata Yi Aiki da Tinubu Don Biyan Basussuka – Akpabio
Dan takarar sanata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi alkawarin cewa majalisar dattawa ta 10 za ta hada kai da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wajen biyan basussukan da ake bin kasar, The Nation ta rawaito.
Akpabio ya yi wannan alkawarin ne a wata ganawa da ya yi da kungiyar Sanatocin APC masu zaman kansu a Abuja.